Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu.


Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu.

<!-- IMAGE -->

Na biya a mace-macen mata a kasashe masu tasowa da ma Duniyar baki daya ita ce Nijeriya, inda a cikin mata masu juna biyu 200,0000, wajen 75,000 ne ke rasuwa sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa.

Ma'ana, kullayaumin mata 230 na mutuwa sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa ko kuma a kowane awa daya mata 6 na mutuwa saboda lalurorin ciki ko haihuwa a Nijeriya.

Idan kuma mun mai da hankali kan Nijeriya, sai kuma mu ga cewa al'amarin ya fi karfi a Arewacin kasar, kuma a Arewar ma an fi samun matsalar ta mace-macen mata masu ciki ko haihuwa a Arewa maso gabas.

Matsalar ta mata masu ciki dai na matukar shafar jariransu. Kuma abin ya fi tsanani ne a wuraren da mace-macenna mata ya fi yawa.

Alal misali, a sa'ilinda jarirai 175 ne kadai cikin 150,000 da aka Haifa ke mutuwa a Kudu-maso-yammacin kasar; a Arewa maso gabashin kasar kuwa har wajen 1700 ne ke mutuwa.

To ko mene ne musabbabin yawan mutuwar mata din? Akwai dai dalilai da yawa. Kama daga zuwa asibiti cikin kurarren lokaci, zuwa rashin kyawun hayar zuwa asibitin, zuwa rashin magunguna masu kyau, zuwa rashin kudin zuwa asibitin da kuma wasu al'adun gargajiya masu nasaba da jahilci da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG