Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin zuwa awon ciki yana da yawa.


Muhimmancin zuwa awon ciki yana da yawa.
Muhimmancin zuwa awon ciki yana da yawa.

<!-- IMAGE -->

Zuwa awon ciki ga mai juna biyu yana da matukar muhimmanci ga samun haihuwa lafiya cikin yardan Allah madaukakin Sarki.

Farkon abubuwan da ake yiwa ga sababbin zuwa, shine auna fitsari da jinni don a tantance lafiyar mai ciki da nufin gano ko tana da wasu cutukan da zasu iya kawo mata matsala idan ta zo haihuwa.

Misali ana gano alamomin ciwon kumburi da ciwon suga ta gwajin fitsari. Sanin kowa ne cewa ciwon kumburi ga mai juna biyu yana haddasa mutuwa in da karar-kwana. Ana kuma gano su ciwon sanya da makamantansu.

A wajan gwanda jini, ana gano alamun kwayar cutar HIV mai karya garkuwan jiki, ana gano adadin yawan jini a jikin mai juna biyu, domin karancinsa yana da illa. Shi yake sa mai ciki ta rika fama da azababben ciwon kai, daga nan ya kawo hawan jinni, a karshe kuma ya haddasa ciwon jijjiga ko tsikau-tsinkau a lokacin nakuda. In ba'a je asibiti da wuri ba, ana iya rasa mai juna-biyu da jaririnta.

Da zarar an gano cutuka, ana baiwa mai lalurar magunguna don a warkar da cutukan da aka gano kafin lokacin haihuwa ta zo.

Misali masu hawan jini, ana basu magunguna tare da hana su cin gishiri, su kuma masu karancin jini, ana fada masu irin ganyayyakin da zasu rika ci masu kara jini, masu cutar HIV ko kanjamau, ana basu maganin da zai rage kaifin ciwon tare da wanda zai kare jaririn dake cikin mahaifa daga harbuwa da cutar HIV.

A wajan awon ciki, ana baiwa mata maganin rigakafin zazzabin cizon sauro wanda ke saurin hallaka mata masu juna biyu da jarirai 'yan kasa da shekara biyar (5) da haihuwa. Don haka, ya ku dangi kada a shagala, mu tura matanmu da yayanmu zuwa awon ciki akan kari.

Ana fara zuwa awon ciki daga wata uku zuwa hudun idan an makara ken nan. Sau hudu kachal ake zuwa awo kafin haihuwa sai dai in akwai lalura mai karfi, ma'aikatan asibiti na iya fada wa mace lakacin da zata koma asibitin don a duba lafiayarta.

XS
SM
MD
LG