Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kawancen Najeriya Da Amurka


Sabon Kawancen Najeriya Da Amurka
Sabon Kawancen Najeriya Da Amurka

<!-- IMAGE -->

A ranar talata Amurka da Najeriya suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar kafa wata Hukumar Kasa ta tuntubar juna da nufin taimakawa Najeriya wajen inganta yadda ake mulkin kasa da yaki da zarmiya da cin hanci. Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta bayyana dangantakar Amurka da Najeriya a matsayin mai matukar muhimmanci.

Wannan yarjejeniya, wadda sakatariya Clinton da sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya, Yayale Ahmed, suka rattaba ma hannu, zata kafa hukumar tuntubar juna ta hadin guiwa ta farko daga cikin guda uku da gwamnatin shugaba Barack Obama take da niyyar kafawa da wasu muhimman kasashen Afirka. Nan bada jimawa ba ake sa ran kammala yarjejeniyar kafa irin wannan hukuma da kasashen Afirka ta Kudu da Angola.

Hukumar Tuntubar ta Amurka da Najeriya zata kasance tana da wasu kwamitoci na musamman wadanda za a dora ma alhakin taimakawa Najeriya wajen yakar zarmiya da magudin zabe, da shawo kan matsalolin noma da rashin wutar lantarki da mai a cikin gida, da kuma kawo karshen fitina a yankin Niger Delta mai matukar muhimmanci ga kasar.

A furucinta lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Clinton ta ce ci gaba da bunkasar tattalin arzikin Najeriya da wasu wuraren, ya dogara a kan gwamnati mai adalci wadda zata yi watsi da zarmiya ta tabbatar da yin mulki bisa doka. A lokacin da take magana game da rikicin siyasar Nijeriya mai alaka da doguwar jinyar da shugaba Umaru Yar’aduwa yake yi, Clinton ta yaba da irin juriyar da shugabannin kasar suka nuna, tana mai cewa, "Na sani da kai na cewa ‘yan Nijeriya masu kuzari da karfin zuciya da juriya da kuma basira ne. Amma shekarar da ta shige ta zamo wadda ta gwada juriyar ‘yan Nijeriya. Muna karfafa guiwar shugabannin Nijeriya da su ci gaba da yin aiki tare wajen takalar rashin sanin tabbas na siyasa, da karfafa cibiyoyin dimokuradiyya tare da tabbatar da kwanciyar hankali da gaskiya."

Alhaji Yayale Ahmed, wanda tsohon ministan tsaro ne na Nijeriya, yace kasarsa tana fuskantar munanan matsaloli, amma wadanda za a iya shawo kansu, kamar yadda aka gani lokacin da majalisar dokoki ta nada Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa na riko a watan da ya shige. Yayale Ahmed ya ce, "Kasancewar mun tsallake watanni kalilan da suka shige a zaman kasa kakkarfa, ta nuna cewa dimokuradiyyarmu ma ta yi karfi. Na yi imani da cewa babu wata kasa a Afirka da zata iya shiga halin da Nijeriya ta shiga ta fito kamar yadda Nijeriyar ta fito."

Sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriyar yayi marhabin da shawarar da gwamnatin shugaba Obama ta dauka a makon jiya, ta soke shirin nan na yin binciken kwakwaf a kan duk wani dan Nijeriya da na wasu kasashen Musulmi 13 idan suka zo shiga jirgi zuwa nan Amurka. Yayale Ahmed yace tsarin ware ‘yan Nijeriya ana yi musu binciken kwakwaf tamkar cin zarafin Nijeriya ne domin kasar ba ta da wani tarihi na ta’addanci, kuma tana kokarin zamowa muhimmiyar kawa ga Amurka wajen yakar ta’addanci a duniya.

XS
SM
MD
LG