Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutanen Goma sunyi Kunnen Uwar Shegu - 2002-01-21


Dubban mazauna yankin garin Goma na Congo wadanda aman wutan dutse ya kawar, suna neman kewaya wani fili da har yanzu ruwan dutsen mai ci gaba da hucin zafi ya kwanta, suna neman isa ga gidajensu, duk kuwa da gargadin da ake ci gaba da yadawa cewa iskar dake yankin tana tattare da guba da kuma yiwuwar yada cututtuka. Jami’an MDD sun bukaci ‘yan gudun hijirar da aka kiyasta cewa sun kai dubu 300 da su tafi sansanonin ‘yan gudun hijirar ne dake kusa da Rwanda. Suka ce iskar dake Goma ta rigaya ta gurbata kuma tana tattare da guba mai cutarwa. Ruwan dutse mai zafin gaske da ya rika kwaranya ya rigaya ya kawarda dukkan kafofin tsaftace ruwan sha, sannan ruwan da yayi saura na wani tabki shi ma ya gurbace. Jami’an suka ce amfani da ruwan tabkin na iya kawo bullar cutar amai da zawo. Amma wasu ‘yan gudun hijirar suka ce gara su fuskanci matsalar cututtukan da zaman sansanin gudun hijijra na MDD. A halinda ake ciki kuma, dutsin dake amai - dutsin Nyirangongo -- yana ci gaba da tsuma da gurnani tareda fidda hayaki ta ka, bayanda a ranar Alhamis ya fara aiyana fushinsa ta hanyar bindiga. Ya zuwa yanzu mutanen da aka kiyasta sun mutu sun kai 45.

XS
SM
MD
LG