Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe Mayakan al-Qa'ida A Wata Gwabzawa - 2002-01-24


Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon sunce an kashe akalla mayakan kungiyar al-Qa'ida goma sha biyar kuma wani sojan Amirka ya dan samu rauni a sakamakon musayar harbe harben da aka yi. Haka kuma sun baiyana cewa an kama ’yan al-Qa'ida ashirin da bakwai, an kai su birnin Kandahar domin yi musu tambayoyi. Shi ma sojan an dauke shi.

Sakataren tsaron Amirka, Donald Rumsfeld, ya fadawa manema labaru anan birnin Washington DC cewa, wannan al'amari ya faru ne a lokacin da aka kai sumame gidajen ’yan al-Qa'ida kimanin kilomita dari daga arewacin Kandahar. Ya jaddada furucinsa na farko cewa har yanzu ana samun bijirewa a Afghanistan duk da yunkurin da Amirka ke yi na kamawa, ko kuma kashe dukkan ’yan kungiyar al-Qa'ida dake boye a kasar.

Yace za’a ci gaba da kai irin wannan sumame lokaci- lokaci.

XS
SM
MD
LG