Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Sudan Suna Zargin Gwamnati - 2002-01-24


Babbar kungiyar 'Yan-tawayen Sudan (S-P-L-A) ta zargi gwamnati da laifin saba wata yarjejeniyar tsagaita wuta, wadda ta fara aiki shekaranjiya talata a tsaunukan Nuba, dake yankin tsakiyar kasar. Dakarun na S-P-L-A, sun ce sun kashe wasu sojojin gwamnati guda shida, a wani farmaki da bangaren gwamnatin ya kai jiya laraba a kan sansanin 'yan tawaye dake Tulushi.

‘Yan-tawayen, sun ce, an kuma kashe biyu daga cikin askarawansu, aka jikkata wasu su bakwai.

Gwamnatin Sudan ba ta mayar da martani ga wannan sanarwa da ‘yan-tawayen suka bayar ba, wadda babu wata majiya mai zaman kanta da ta iya tabbatar da ita.

A ranar asabar din da ta gabata ce, gwamnati da ‘yan-tawayen na Sudan su ka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, a wata tattaunawa da kasashen Amurika da Switzerland suka shiga tsakani wajen gudanar da ita.

An cimma wannan dawajewa ce, da nufin bada sukunin kai gudumawar jinkai ga mazauna lardin tsaunukan na Nuba. Kodayake, ‘yan-kallo na kasa da kasa ya kamata su lura da wannan yarjejeniya, amma haryanzu ba su isa wannan yanki ba.

XS
SM
MD
LG