Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Nijeriya Sun Gwabza Da Masu Zanga-Zanga - 2002-01-26


‘Yan sandan Nijeriya sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa zanga-zangar da ta barke jiya Jumma’a a kusa da babbar kasuwar Wuse a Abuja, babban birnin kasar. Shaidu sun ce an ji rauni ma ’yan sanda da masu zanga-zanga da dama a wannan arangama.

Wakilin Muryar Amurka a Abuja ya ce masu zanga-zangar sun far wa motoci da dama, ciki har da na ’yan sanda. ‘Yan sanda ba su ce uffan kan wannan ba.

Wannan zanga-zanga da tarzoma sun barke a bayan da jami’an babban birnin tarayya suka yi kokarin rushe kantunan da aka kakkafa ba tare da izni ba. Masu kantunan sun ce hukumomin birnin ne suka rushe musu tsoffin kantunansu tun farko.

XS
SM
MD
LG