Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Suna Ci Gaba Da Yin Zanga-Zanga a Madagascar - 2002-01-29


Magoya bayan ’yan adawa sun shiga kwana na biyu da fara zanga-zanga a Antananarivo,babban birnin kasar Madagascar, da nufin tilastawa gwamnatin kasar ta sauka daga kan mulki.

Shaidu sun ce an rufe kantuna da cibiyoyin hada-hadar kasuwanci, sannan suka ce an dakatar da motocin safa, haka nan ma a babban filin jirgin saman birnin komi ya tsaya cak a daidai lokacin da dubban daruruwan mutane su ka yi dandazo a babban dandalin birnin domin nuna goyon baya ga yadda komi ya tsaya cak.

Dan takarar shugaban kasar ’yan adawa, Marc Ravalomanana, wanda kuma har ila yau shi ne magajin garin birnin Antananarivo, ya yi kiran a yi zanga-zanga ta sai illa masha’Allahu domin a yi matsin lamba ga gwamnatin kasar ta yi murabus bayan zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan Disemban bara wanda ya yi ikirarin lashewa.

Mr. Ravalomanana ya yi fatali da hukumcin madaukakiyar kotun tsarin mulkin kasar, wadda ta ba da umarnin yin zagaye na biyu, sannan kuma ya zargi hukumomi da tafka magudi a zaben domin su baiwa shugaba Didier Ratsiraka damar lashe zaben.

XS
SM
MD
LG