Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fadada Neman Dan Jaridar Da Aka Sace a Pakistan - 2002-02-04


'Yan-sandan Pakistan sun fadada neman da suke yi na Ba’amuriken nan dan jarida da aka sace, ya zuwa dukkan lardunan kasar ta Pakistan guda hudu. Hukumomi sun fada yau litinin cewa, yanzu binciken da suke yi na gano Daniel Pearl, wakilin jaridar Wall Street Journal, wanda aka sace a ranar 23 ga watan jiya na Janairu, ya zarta Karachi, birni mai tashar jiragen ruwa a kudancin kasar ta Pakistan.

'Yan-sandan suna kuma kokarin sanin walau akwai hannun wasu kungiyoyi ‘yan-bindiga wajen sace Mr. Pearl.

Kodayake hukumomin na Pakistan sun ce babu wata alama mai basu wata masaniya gameda inda wannan dan jarida yake a halin yanzu, amma kuma sun yi nunin cewa, suna samun ci gaba a binciken da suke gudanarwa.

Wata gawa da aka tsinta jiya lahadi, da farko an bada rahotan cewa ta Mr. Pearl ce, amma daga baya sai aka fahimci cewa, ba ta wannan Dan-jarida ba ne da aka sace.

XS
SM
MD
LG