Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kai Hari Kan Cibiyar Tsaron Falasdinawa - 2002-02-15


Jiragen saman yaki na Isra’ila sun kai hari kan wani gini na jami’an tsaron Falasdinawa a zirin Gaza, a bayan koma-bayan da Isra’ilar ta samu a fagen ayyukan soja a Gaza da yankin yammacin kogin Jordan.

Falasdinawa sun ce wadannan hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai a arewa da birnin Gaza, sun raunata mutane akalla 16, daya daga cikinsu kuwa rauni mai tsanani.

Tun da fari a jiya Jumma’a an kashe kwamandan wata runduna ta zaratan sojojin Amurka lokacin da suka kai farmaki kan wani kauyen falasdinawa dake yankin yammacin kogin Jordan.

A daren alhamis, wani bam da Falasdinawa suka dasa ya ragargaza wata tankar yaki ta Isra’ila a Gaza, ya kashe sojoji uku dake ciki.

XS
SM
MD
LG