Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Shugaban Adawa Na Zimbabwe Da Laifin Cin Amanar Kasa - 2002-02-25


Babban madugun adawa na kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya ce an tuhume shi da laifin cin amanar kasa bisa zargin da aka yi cewar ya kulla makarkashiyar kashe shugaba Robert Mugabe.

Mr. Tsvangirai ya musanta wannan zargi a gaban 'yan jarida, bayan da 'yan sanda suka yi masa tambayoyi yau litinin a hedkwatarsu dake birnin Harare. Tuhumarsa da aka yi yau, wadda hukumcinta kisa ne, ta zo makonni biyu kafin a gudanar da zaben shugaban kasar da shine babban mai kalubalantar shugaba Robert Mugabe.

Gwamnati ta ce madugun 'yan adawar ya gana da wata kungiyar bada shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Canada, inda ya shirya yadda za a kashe Mr. Mugabe. An nuna faifan bidiyo na wannan ganawa tasu a gidan telebijin na kasar, koda yake da alamun an yayyanke wasu sassan faifan da dama.

Mr. Tsvangirai ya ce sharri kawai wannan kungiyar bada shawara ta kulla masa, yana mai bayyana wannan faifan bidiyo a zaman yunkuri na gurgunta shirin yakin neman zabensa.

A can baya ma, an taba yi wa madugun adawar barazanar tuhuma da laifin cin amanar kasa.

Shugaban na jam'iyyar adawa ta MDC zai fuskanci shugaba Mugabe a zaben shugaban kasa a ranakun 9 da 10 ga watan Maris.

XS
SM
MD
LG