Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Zai Gana Da Wasu Shugabannin Afirka Uku - 2002-02-26


A yau talata shugaba Bush zai gana a nan Washington da shugabannin wasu kasashe uku na Afirka domin tattaunawar da ake sa ran zata fi mayar da hankali kan batutuwan zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kasashen.

Shugaba Jose Eduardo dos Santos na Angola zai hadu da shugaba Joacquim Chissano na Mozambique da shugaba Festus Mogae na Botswana domin wannan tattaunawa da za a yi a fadar White House.

Ana ganin cewa wannan tattaunawa, wadda aka bada sanarwarta a makonnin baya, ta kara sabon tasiri da muhimmanci a bayan mutuwar madugun 'yan tawayen UNITA, Jonas Savimbi, wanda aka kashe a wata gwabzawa da sojojin gwamnati ranar Jumma'a.

Gwamnatin shugaba Bush ta ce mutuwar Mr. Savimbi ta nuna cewar bukatar wanzar da zaman lafiya a Angola ta zahiri ce. Kungiyar UNITA ta fara yakar gwamnatin Angola tun shekarar 1975.

Har ila yau ana sa ran abubuwan ad shugabannin zasu tattauna kai a yau zasu hada da batutuwan cinikayya da bunkasa tattalin arziki, da kawar da talauci da kuma yaki da cutar kanjamau ta AIDS ko SIDA.

A lokacin da ya ziyarci Portugal a ranar litinin, shugaba dos Santos na Angola yayi kiran da a tsagaita wuta a tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen UNITA a kasarsa. Ya shaidawa 'yan jarida cewar yana son ya dauki matakan hamzari na daidaita al'amuran siyasa a kasar tasa.

Har ila yau shugaban na Angola ya ce yana sa ran gudanar da zabe cikin shekaru biyu a kasar, amma kuma wannan ya dogara ne kan cimma shirin vtsagaita wuta da kuma kwance damarar yaki na kungiyar UNITA.

Amma kuma 'yan tawayen UNITA sun ce zasu ci gaba da yakar gwamnati.

XS
SM
MD
LG