Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Nemi Da A Tsagaita Wuta A Angola - 2002-02-27


Shugaba Bush ya bukaci da a tsagaita bude wuta a yakin da ake fafatawa a kasar Angola, a yayinda yayi kira ga shugaban kasar, Jose Eduardo Dos Santos, da yayi amfani da wannan dama daya samu ta mutuwar madugun 'yan tawayen UNITA, Jonas Savimbi, wajen kawo karshen yakin shekaru ashirin da shidda a kasar.

A jiya talata shugaba Bush yayi wannan kira, bayan ya gana da shugaba Dos Santos da wasu shugabanin kasashen Afrika guda biyu, Joacquim Chissano na Mozambique da Festus Mogae na Botswana. Mr. Bush yace alhaki ne daya rataya akan dukkan bangarorin Angola suyi amfani da wannan dama domin kawo karshen yakin basasar kasar da kuma inganta albarkatunta ta yadda dukkan 'yan Angola zasu ci moriya.

Mr. Dos Santos ya fadawa 'yan jarida cewa ya kosa da yaga an tsagaita bude wuta nan bada jimawa ba. To, amma kuma, yace samun wanzuwar haka zai dogara ne akan abinda ya kira aniyar harkokin siyasa da 'yan tawayen kungiyar UNITA ta Angola zasu kudurta.

Tun a 1975 kungiyar UNITA take fafatawa da gwamnatin kasar ta Angola. Wannan rikici ya sa miliyoyin jama’a sun yi hasarar gidajensu, yayin da wasu dubban mutanen suka rasa rayukansu.

A makon jiya aka kashe Mr. Savimbi a arangama da sojojin gwamnati.

A harin farko da aka bada rahotonsa tun kashe Savimbi da aka yi, 'yan tawayen kungiyar UNITA sun kashe mutum tara suka raunata wasu goma sha biyar a wani hari da aka kai a tsakiyar Angola a shekaranjiya litinin.

Ganawar da shugaba Bush da shugabannin Afrikan guda uku suka yi, ta mayar da hankali akan hanyoyin bunkasar tattalin arziki da samun wanzuwar zaman lafiya a yankinsu. Mr. Bush ya ce fadada harkokin cinnikayya itace hanyar data fi dacewa ta tabbatar da bunkasar tattalin arziki a yankin.

XS
SM
MD
LG