Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkalan Scotland Sun Yi Watsi Da Daukaka Karar Dan Kasar Libya - 2002-03-14


Wata kotun Scotland ta musamman dake yin zama a Netherlands ta tabbatar da hukumcin da tun farko aka yanke kan wani jami'in leken asirin kasar Libya, na daurin rai da rai a kurkuku dangane da dasa bam cikin wani jirgin saman fasinja na Amurka da ya tarwatse a samaniyar Lockerbie, a Scotland, a shekarar 1988.

Dukkan alkalai 5 da suka saurari batun sun yi watsi da daukaka karar Abdel Basset Ali al-Megrahi, wanda a shekarar da ta shige kotun ta same shi da laifin dasa bam cikin akwatin kaya, wanda kuma ya fashe a sama cikin jirgin kamfanin Pan Am, ya kashe mutane 270.

Masu gabatar da kara sun ce an dasa wannan bam cikin akwatunan da aka yi lodi a filin jirgin saman tsibirin Malta, daga baya aka maida akwatin dake dauke da bam din cikin wannan jirgi da ya tarwatse ya subuto kasa.

A lokacin da suke gabatar da hujjojinsu na daukaka kara, lauyoyin al-Megrahi sun gabatar da shaidu an gani da ido, wadanda suka bada shaidar cewa kwana guda kafin fashewar wannan jirgi a sama, an fasa aka shiga cikin wurin ajiye akwatunan kayayyaki na filin jirgin saman Heathrow dake London, inda aka yi ma wannan jirgi lodi. Suka ce wannan shaida ta janyo tababa game da ikirarin masu gabatar da kara cewa al-Megrahi ne ya dasa bam din.

Kotun dai tun farko ta saki mutumi na biyu da aka tuhuma tare da al-Megrahi, watau Al-Amin Khalifa Fahima.

XS
SM
MD
LG