Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gambari ya baiyana shirin Angola bayan mutuwar Jonas Savimbi - 2002-03-21


Jiya (Laraba) a birnin New York babban jami'i na musamman mai baiwa shugaban Majalisar Dinkin Duniya shawara kan harkokin Afirka, Ibrahim Gambari ya baiyanawa wakilan taron cewa akwai alamun samun kwanciyar hankali a Angola. Shi dai jami'i Gambari ya gabatarda wani shiri dalla dalla mai sassa 15 da gwamnatin kasar ta samar da nufin tabbatarda wanzarda zaman lafiya, ciki harda dakatarda dukkan hare hare da kuma amincewa komawa ga bin sharuddan wani shirin da aka taba amincewa tsakanin gwamnatin da 'yan tawaye a Lusaka, wanda akafi sani da suna "Lusaka Protocol." Haka shirin ya kuma hada da gagarumin matakin agajin jin kai ga al'umar kasar. Mr Gambari ya ce mutuwar da madugun 'yan tawaye Jonas Savimbi yayi a kwanan nan ya zama muhimmin matsayinda ya kyautata yiwuwar samun zaman lafiya. Gambari ya baiyana cewa "Dama dai Savimbi ke zaman kayan wuya ko kadangaren bakin tulu. Kawarda shi ya samarda wata dama ta iya ciyarda shirin na zaman lafiya a gaba." Haka Jami'i Gambari ya ce shi dai fatarsa ita ce gwamnatin ta Angola zata tashi tsaye wajen amfani da damar da ta samu. Ya kuma karkare da cewa, domin ganewa idonsa abinda ke aukuwa acan Angola a zahiri, zai koma can, inda ya ce har yanzu ana fama da "wata matsalar tagaiyara mawuyaciya."

XS
SM
MD
LG