Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Sojan Sama Na Amurka Da Laifin Yin Fyade a Okinawa - 2002-03-28


Wata kotun kasar Japan ta samu wani sojan saman Amurka da laifin yin fyade ma wata mace 'yar kasar Japan, ta kuma yanke masa hukumcin daurin watanni 32 a kurkuku.

A yau alhamis wannan kotu dake tsibirin Okinawa ta samu Saje Timothy Woodland, da wannan laifin.

An gurfanar da Woodland a gaban kotu a watan Satumba, a bayan da aka tuhume shi da yin fyade ma wata mace mai shekaru 20 da haihuwa a garejin ajiye motoci dake kofar wani shahararren gidan rawa.

Woodland ya yarda cewa ya tara da wannan mace, amma kuma ya ce da yardarta.

Masu gabatar da kararraki sun bukaci da a daure Woodland na tsawon shekaru uku. Wannan shari'a ta kara rura wutar kiyayyar sojojin Amurka a Okinawa. Akwai dubban sojojin Amurka a wannan tsibiri na kasar Japan.

XS
SM
MD
LG