Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bani Isra'ila Na Ci Gaba Da Killace Yasser Arafat - 2002-04-01


Har yanzu ana cigaba da killace shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a cikin hedkwatarsa dake birnin Ramallah, a yankin Yammacin kogin Jordan.

Malam Arafat, wanda a halin yanzu dakarun Isra'ila suka yi masa kofar rago, ya ce yana jin rayuwarsa na cikin hatsari.

Babban jami'in shawarwarin Falasdinawa, Saeb Erekat, ya ce sojojin Isra'ilar suna dab da dakin da Malam Arafat yake, harma yana jin suna magana da harshen yahudanci.

Duk da haka, jagoran na Falasdinawa ya tsaya kai da fata akan matsayinsa, yana yin kira ga kasashen duniya da su tursasawa dakarun Isra'ilar su janye.

A jiya lahadi, wata kungiyar nuna kyama ga rikice-rikice daga kasashen yamma, ta shammaci tankokin yakin Isra'ila da dakarun dake tsaron Malam Arafat, ta shiga wannan hedkwata, ta gana da Malam Arafat.

Wakilan kungiyar sun ce za su cigaba da zama da jagoran Falasdinawan, domin su ba shi kariya daga dukkan wani farmaki.

An bada rahotan cewa, wannan kungiya ta 'yan rajin zaman lafiya ta kunshi akalla wani mutumin Isra'ila guda daya, da Faransawa, da Jamusawa da kuma wasu Amurkawa.

Tuni dai Isra'ila, ta ayyana birnin Ramallah a matsayin wani yankin soji da aka kulle, sannan ta umarci dukkan 'Yan-jarida su fice daga birnin.

XS
SM
MD
LG