Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Sun Ce Isra'ila Ta Shiga Cikin Bethlehem - 2002-04-02


Falasdinawa da suka ganewa idanunsu, sun ce tankokin Isra'ila sun kutsa har cikin tsakiyar birnin Bethlehem a ci gaba da fadada kyamfe din ad Isra'ila ta kaddamar a yankin Yammacin kogin Jordan.

Shaidu sun ce tankokin Isra'ila sun kutsa har dab da majami'ar nan ta Bethlehem da ake kira "Church of the Nativity" inda a bisa al'ada aka ce an haifi Annabi Isa Alaihis Salam.

A yau talata ne kuma Falasdinawa suka ce sojojin Isra'ila sun shiga sansanin 'yan gudun hijira na Dheishe dake kusa da nan. A jiya litinin, tankoki da sojojin Isra'ila sun shiga cikin garuruwan Tulkarem da Bethlehem, a bayan da suka sake mamaye Qalqiya da maraicen lahadi.

A can Ramallah kuma, babban jami'in tsaron Falasdinawa, Jibril Rajoub, ya ce fada ya barke a ofishinsa, ya kuma ce sojojin Isra'ila suna yin amfani da Falasdinawa a zaman garkuwa a yayin da suka tinkari ofishin. Jami'an Isra'ila sun ce ba haka ba ne.

Mr. Rajoub ya ce an rutsa da Falasdinawa su 400 a ofishinsa, yayin da Isra'ila take cewa tana neman da yawa daga cikinsu saboda kitsa hare-hare kan Isra'ila.

Har ila yau a can Ramallah, ana ci gaba da killace shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, a hedkwatarsa, inda tun ranar Jumma'a sojojin Isra'ila suka kawanya wa ginin.

XS
SM
MD
LG