Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tankokin Yakin Isra'ila Sun Shiga Jenin Da Salfeet - 2002-04-03


Shaidu sun ce tankokin Isra'ila sun shiga cikin garuruwan Falasdinawa na Jenin da Salfeet a arewacin yankin Yammacin kogin Jordan.

Tankokin sun kutsa cikin wadannan garuruwa a yau laraba, a matakin baya-bayan nan na yadda Isra'ila take kara fadada farmakin da ta shafe kwana shida tana kaiwa Falasdinawa mayakan sakai.

An bada rahoton cewa dakarun Isra'ilar sun fuskanci barin wuta babu kakkautawa daga Falasdinawa a birnin Jenin, amma na Salfeet kuwa sun shiga salun alun.

A can birnin Bethlehem kuwa, gungun Falasdinawa 'yan bindiga wadanda suke fafatawa da sojojin Isra'ila sun ci gaba da tarewa a cikin cocin da bisa al'ada aka ce can ne aka haifi Annabi Isa Alahis-salam.

'Yan-bindigar sun fake a wannan wuri mai tsarki ga Kiristoci, wasu sa'o'i bayan fafata yaki jiya talata.

XS
SM
MD
LG