Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharon Ya Nuna Cewar Akwai Sabanin Ra'ayi Tsakaninsu Da Amurka - 2002-04-08


Firayim ministan Isra'ila Ariel Sharon ya watakila akwai abinda ya kira "sabanin ra'ayi" tsakaninsu da Amurka kan matakan sojan da Isra'ila take dauka a yankin Yammacin kogin Jordan, farmakin da shugaba Bush ya ce ya kamata a kawo karshensa ba tare da jinkiri ba.

Mr. Sharon ya ce tilas a ci gaba da kai wannan farmaki har sai sun zakulo 'yan kishin Falasdinun dake da hannu a hare-haren bam na kunar-bakin-wake da ake kaiwa kan Isra'ila.

A jiya lahadi, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya tattauna farmakin da Isra'ila take kaiwa a yankin Yammacin kogin Jordan. Jami'an Falasdinawa da na Larabawa sun yi kiran da a gaggauta aiwatar da kudurin MDD wanda ya bukaci Isra'ila ta janye nan take.

Mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan harkokin tsaron kasa, Condoleeza Rice, ta ce bai kamata Isra'ila ta jira isar sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, a birnin al-Qudus cikin makon nan kafin ta fara janyewa ba.

XS
SM
MD
LG