Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Suna Ci gaba Da kai Farmaki a Kan Falasdinawa - 2002-04-08


An ji karar harbe-harbe yau litinin da safiya a kewayen majami'ar nan ta "Church of the Nativity" a birnin Bethlehem, yayin da a can arewa a cikin yankin Yammacin kogin Jordan jiragen saman yaki masu saukar ungulu na Bani Isra'ila suka cilla rokoki kan sansanin Falasdinawa 'yan gudun hijira dake Jenin.

Rahotanni daga Bethlehem sun ce wuta ta barke cikin wani gini dake kusa da wannan majami'a, inda kiristoci suka yi imanin an haifi Annabi Isa (Alaihis Salam), yayin da aka ji karar harbe-harbe a yankin. Wata majiyar Falasdinawa ta ce sojojin Isra'ila sun bindige suka kashe wani Bafalasdine a wurin.

Har yanzu akwai Falasdinawa su kimanin 200, wasunsu dauke da bindigogi, boye cikin wannan majami'a, inda suka nemi mafaka a ranar talata.

A halin da ake ciki, jiragen saman kai farmaki na sojojin Isra'ila sun yi ta luguden wuta kan sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, a bayan da suka umurci Falasdinawan dake can da su mika kai.

Shaidu sun ce makamai masu linzami akalla 15 ne suka abka kan sansanin a safiyar yau litinin.

XS
SM
MD
LG