Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Suna Janyewa Daga Wasu Birane Biyu A Yammacin Kogin Jordan - 2002-04-09


Gidan rediyon Isra'ila da kuma majiyoyin tsaro na Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun fara janyewa daga biranen Falasdinawa na Qalqiliya da Tulkarem.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta bayyana wannan 'yar takaitacciyar janyewa daga biranen Falasdinawa da Isra'ila ta mamaye a zaman "mafari."

Amma kuma janyewar, ko kusa, ba ta kai kiran da shugaba Bush yayi ma Isra'ila jiya litinin cewar ta janye sojojinta daga dukkan biranen Falasdinawa da ta mamaye ba tare ad wani jinkiri ba.

A can kasar Morocco, sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya ce yana fata wannan mataki na Isra'ila matakin farko ne na janyewa gadan-gadan. Yayi magana a bayan da ya gana da Sarki Muhammad na Morocco da Yarima Abdullahi mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya.

Sarki Muhammad na Morocco ya shaidawa Mr. Powell cewa wannan ziyara tasa zata fi yin tasiri idan da ya faro ta, ko ya wuce kai tsaye, zuwa birnin Qudus. Amma Mr. Powell ya ce yana son tuntubar shugabannin Turai da na Larabawa kafin ya je shi Isra'ila ranar Jumma'a.

Biranen Qalqiliya da Tulkarem suna cikin garuruwan farko na Falasdinawa da Isra'ila ta kai wa farmaki domin zakulo abinda ta kira 'yan ta'adda.

A lokacin da yake yin ko oho da rokon kasashen duniya, firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila ya shaidawa majalisar dokokinsa cewar za a ci gaba da farmakin da ake kaiwa a yankin Yammacin kogin Jordan har sai an murkushe dukkan 'yan ta'adda.

XS
SM
MD
LG