Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kwango-Kinshasa Ta Bai Wa 'Yan Tawaye Mukamin Firayim Minista - 2002-04-10


Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyya ta Kwango, kasar da yaki ya tagayyara, ta ce a shirye take ta damka mukamin Firayim Minista ga wani madugun 'yan tawaye, a gwamnatin wucin gadi da za a kafa, amma kuma ta ce za ta cigaba da rike mukamin shugaban kasa.

A jiya talata ne, gwamnatin ta Kwango-Kinsasha ta gabatar da wannan shawara, a daidai lokacin da ake samun tafiyar hawainiya a tattaunawar da ake yi a birnin Sun City na Afrika ta Kudu, da nufin kawo karshen yakin da aka shafe kusan shekaru hudu ana fafatawa a Kwangon.

Yayin da jami'an gwamnatin Kwangon suka tsaya kai da fata cewa, shugaba Joseph Kabila ya cigaba da zama kan karagar mulki har sai an gudanar da sabon zabe, babbar kungiyar 'yan tawayen kasar mai babatun tabbatar da dimokuradiyya, ta yi fatali da lamarin.

Kungiyar ta ce, akwai wata matsala gameda halascin Mr. Kabila wanda ya gaji mahaifinsa da aka kashe bara, ya ci gaba da mulki.

XS
SM
MD
LG