Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Likitan Mutuwa' Na Afirka ta Kudu Zai Fuskanci Hukumci Yau Alhamis - 2002-04-11


A yau alhamis ake sa ran wata babbar kotun Afirka ta Kudu a birnin Pretoria za ta yanke hukumci kan Wouter Basson, shugaban wata hukumar binciken yin amfani da kwayoyin cuta a zaman makami a lokacin mulkin wariyar launin fata, wanda ake zargi da aikata laifuffuka 46, cikinsu har da kisan kai, da kulla makarkashiya, da zamba da kuma mallakar magunguna.

Dr. Basson, wanda kafofin yada labaran Afirka ta Kudu suke kira "Likitan Mutuwa" ya ce bai aikata ko guda daya daga cikin laifuffukan ba.

Lauyoyin gwamnati sun tuhumi Dr. Basson, likitan ciwon zuciya, da laifin hada guba ta musamman domin kashewa, ko kuma yunkurin kashe masu adawa da gwamnatin turawa 'yan wariyar launin fata, akasarinsu bakaken fata.

Har ila yau, an zarge shi da laifin sace miliyoyin daloli daga wani shirin gwamnati na sirri na harhada makamai da kwayoyin cuta wanda ake kira "Project Coast" domin gudanar da rayuwa irinta annashuwa tare da yin tafiye-tafiye a fadin duniya.

A lokacin wannan shari'a ta tsawon shekaru biyu da rabi, shaidu sun ce a shekarun 1980 da kuma farko-farkon shekarun 1990, Dr. Basson yayi aikin samo hanyar da ta fi sauki ta kashe masu yin adawa da mulkin wariyar launin fata.

Idan har aka same shi da laifi, yana iya fuskantar daurin rai da rai a gidan katso.

XS
SM
MD
LG