Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Shida Sun Mutu A Hadarin Jirgin Kasa A Amurka - 2002-04-19


Mutane akalla 6 sun mutu, wasu 75 suka ji rauni, cikinsu har da mutane 20 da suka ji rauni mai tsananin gaske, a lokacin da wannan jirgin kasa mai farin jini a wurin fasinja ya zame daga kan layin dogonsa a Jihar Florida a gabashin nan Amurka.

Taragai har 17 na jirgin sun yi juyin waina, jim kadan a bayan da wannan jirgin kasa ya bar garin Sanford a Jihar Florida, kan hanyarsa at zuwa Lorton a Jihar Virginia, kusa da nan birnin Washington DC.

Ma'aikatan agaji suna ci gaba da kokarin zakulo mutane har 75 wadanda suke ritse cikin taragan jirgin.

Masu bincike na tarayya sun doshi wurin hatsarin.

Wannan jirgin kasa, yana daukar fasinjoji da motocinsu a tsakanin Jihar Virginia da kuma wuraren yawon shakatawa na Jihar Florida.

XS
SM
MD
LG