Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Zata Tsinke Huldar Jakadanci Da Isra'ila - 2002-04-22


Jamhuriyar Nijar, wadda ke yankin Afirka ta Yamma, ta ce zata tsinke huldar jakadanci da kasar Bani Isra'ila.

Nijar ta ce ta dauki wannan matakin ne a saboda tsananin "taurin kai da halin ko oho" da firayim minista Ariel Sharon ke nunawa a rikicin da Isra'ila tayi watanni 18 tana yi da Falasdinawa.

A cikin sanarwar da ta bayar lahadin nan, gwamnatin Nijar ta ce firayim ministan na Isra'ila, ya nuna aniya da kuma kwadayinsa na yin watsi da duk irin ci gaban da aka samu a yunkurin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Kasar Nijar, wanda fiye da kashi 90 cikin 100 na al'ummarta Musulmi ne, ta mayar da huldar jakadanci da Isra'ila a shekarar 1996, a bayan da ta tsinke ta a 1973 a bayan yakin Isra'ila da Larabawa.

XS
SM
MD
LG