Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Ta Comoros Ta Soke Sakamakon Zabe - 2002-04-23


Hukumar zabe ta Tarayyar Tsibiran Comoros ta soke sakamakon zaben shugaban kasa na wannan kasa dake tekun Indiya, a bayan da aka yi zargin cewa an tabka magudi.

An gudanar ad wannan zabe ranar 14 ga watan Afrilu, karkashin sabon tsarin mulkin da ya kamata ya maido da zaman tarayya na tsibiran Comoros tare da bai wa tsibiran da suka hadu suka yi wannan tarayya karin ikon cin gashin kai.

Kamfanin dillancin labaran "Associated Press" ya ambaci wani wakilin hukumar zaben, Oukach Mohammed Jaffar, yana fadin cewa soke sakamakon zaben zai ba su damar warware zaman tankiyar siyasa.

Ya gabatar da hujjoji kamar takardun sakamakon zabe masu yawa da babu sa hannu a kai, da rashin 'yan kallo na 'yan takara guda biyu a zaman dalilansu na kin yarda da sakamakon zaben.

Sakamakon farko da aka samu ya nuna cewa tsohon madugun soja kuma shugaban kasa, Azaly Assoumani, shi ya lashe zaben da kashi 75 daga cikin 100.

Biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa, Kanar Mahamoud Mradabi mai ritaya, da Sai Ali Kemal, sun kauracewa zaben, suna zargin yin magudi.

XS
SM
MD
LG