Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obasanjo Zai Sake Yin Takara - 2002-04-26


Shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya ya bada sanarwar cewa zai sake yin takarar wannan mukami a shekarar 2003.

A jiya alhamis, shugaban na Nijeriya ya shaidawa magoya bayansa da suka yi gangami a Abuja, babban birnin kasar, cewa ya cimma wannan shawara, a bayan da ya dauki tsawon lokaci yana shawarwari da "iyalansa, da abokansa, da masu sukar lamirinsa da kuma abokan siyasa."

Ana sa ran gudanar da zaben a cikin watan Afrilun shekara mai zuwa.

An zabi Cif Obasanjo kan wannan mukami a shekarar 1999, a bayan da gwamnatocin soja suka jima suna mulkin kasar.

Masu fashin bakin siyasa sun ce an samu karin 'yancin sakewa da walwala a karkashin gwamnatinsa, koda yake a wani gefen, an samu karuwar tashe-tashen hankula na kabilanci da addini da kuma siyasa.

Cif Obasanjo ya fara mulkin Nijeriya a shekarar 1976 a zaman shugaban soja. Shekaru uku bayan nan, ya mika ragamar mulki hannun zababbiyar gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Aliyu Shagari, ya zamo shugaban Afirka na farko da ya sauka ya mika mulki shi da kansa.

A bayan da ya bar mulki, ya ci gaba da taka rawa a harkokin siyasar kasar.

A shekarar 1983, sojoji sun sake kwace mulkin Nijeriya, har ma Obasanjo ya shiga sahun masu sukar gwamnatocin da suka biyo baya. An yanke masa hukumcin daurin rai da rai a kurkuku, amma sai aka sako shi bayan shekaru uku, a bayan mutuwar shugaban gwamnatin mulkin soja, Sani Abacha a 1998.

Tun daga zabensa ya zuwa yanzu dai, shugaba Obasanjo yana shan suka daga wurin kungiyoyin kare hakkin bil Adama da dama a saboda yadda ya takali wasu tashe-tashen hankulan da suka shafi sojojin kasar.

XS
SM
MD
LG