Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama Ta Ce Ta Ga Shaidar Laifuffukan Yaki A Jenin - 2002-05-03


Wata kungiyar kare hakkin bil Adama mai hedkwata a nan Amurka, ta ce watakila sojojin Isra'ila sun aikata laifuffukan yaki a lokacin da suka kutsa cikin sansanin 'yan gudun hijira na Jenin, amma kungiyar ta ce ba ta ga wata shaida ta kisan gilla ba.

A cikin wani rahoton da za a wallafa a yau Jumma'a, kungiyar "Human Rights Watch" ta ce sojojin Isra'ila sun yi amfani da Falasdinawa fararen hula a zaman garkuwa a lokacin wannan gwabzawa da aka yi a sansanin 'yan gudun hijiran dake Yammacin kogin Jordan.

Rahoton ya ce an kashe Falasdinawa 52 a gwabzawar da aka yi daga gida zuwa gida a cikin Jenin. Kungiyar ta ce 22 daga cikin wadannan mutane fararen hula ne, da yawa daga cikinsu kuwa da gangan aka kashe su ta hanyoyin ad suka saba doka.

Har ila yau Kungiyar ta ce Falasdinawa 'yan bindiga ma sun jefa rayukan fararen hula cikin hadari ta hanyar yin amfani da sansanin a zaman tungarsu.

XS
SM
MD
LG