Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Zata Koma Ga Hidimar Sayarwa Da Kasashen Waje Man Fetur - 2002-05-06


Iraqi ta ce zata koma ga sayarwa da kasashen waje man fetur, wanda ta dakatar wata guda da ya shige domin nuna rashin jin dadin farmakin da Isra'ila ta kai a yankin Yammacin kogin Jordan.

A cikin sanarwar da aka yada ta telebijin na Iraqi, majalisar zartaswar kasar ta ce za a koma ga aikin fitar da man zuwa waje daga karfe goma sha biyun daren laraba, 8 ga watan nan na Mayu.

Sanarwar ta bayyana takaicin cewa sauran kasashen larabawa ba su yi koyi da matakin da Iraqin ta dauka na dakatar da sayarwa da kasashe masu goyon bayan Isra'ila mai ba.

Sanarwar ta ambaci shugaba Saddam Hussein yana fadin cewa talakawa a kasashen larabawa sun goyi bayan wannan mataki da ya dauka, kuma ya dauki wannan takunkumin sayar da mai da ya kafa a zaman wanda yayi nasara.

Takunkumin na Iraqi ya kawar da ganga miliyan biyu na mai a kowace rana daga kasuwannin duniya, sai dai bai yi tasiri kan farashin man ba.

XS
SM
MD
LG