Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Gana Da Shugaba Yoweri Museveni Na Uganda - 2002-05-07


Shugaba Bush ya gana da shugaba Yoweri Museveni na Uganda a nan birnin Washington, domin tattauna zaman lafiya da ayyukan raya kasa a yankin gabashin Afirka.

A bayan ganawar tasu jiya litinin, Mr. Museveni ya shaidawa 'yan jarida cewa sun tattauna batutuwa da dama, ciki har da cinikayya, ta'addanci, da kuma lamarin Kwango Kinshasa.

Mr. Museveni ya ya ce ya fadawa Mr. Bush cewar kasarsa tana kwadayin abinda ya kira "ciniki ka'in da na'in" da Amurka. Ya kuma ce ya fadawa Mr. Bush irin kokarin da ake yi a kasar Kwango Kinshasa, yana mai cewa bangarorin kasar sun yi kusan cimma yarjejeniya.

A lokacin wannan ganaw ta su, Mr. Bush ya taya kasar Uganda murnar namijin kokarin da take yi na yakar cutar kanjamau, watau AIDS.

XS
SM
MD
LG