Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ragargaza Gada Ta 6 A Kasar Madagascar - 2002-05-08


An sake dasa nakiya aka ragargaza wata gadar a kasar Madagascar, a yayin da ake ci gaba da rigimar siyasa tsakanin mutumin da ya jima yana mulkin kasar, shugaba Didier Ratsiraka, da abokin adawarsa, Marc Ravalomanana.

Jami'ai sun ce an dasa nakiya cikin daren litinin, aka lalata wata gadar dake kan wata muhimmiyar hanyar mota a gabashin Madagascar.

Babu wanda ya dauki alhakin dasa wannan nakiya.

Wannan ita ce gada ta shida da aka lalata tun watan Fabrairu, lokacin da Mr. Ratsiraka ya hana komai shiga ko fita daga Antananarivo, tungar babban abokin adawarsa Marc Ravalomanana, wanda a shekaranjiya litinin aka rantsar da shi a zaman sabon shugaban kasar.

Mako guda da ya shige aka ayyana Mr. Ravalomanana a zaman shugaban kasar, bayan da aka sake kidaya kuri'un da aka kada na zaben shugaban kasar. Mr. Ratsiraka ya ki yarda da sake kidaya kuri'un da aka yi, ya kuma bayyana bukin rantsar da sabon shugaban na ranar litinin a zaman na haramun.

XS
SM
MD
LG