Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Tana Shirin kai Farmaki Cikin Zirin Gaza - 2002-05-10


Isra'ila tana sanya sojojinta na wucin-gadi cikin damara, yayin da aka bada rahoton cewa tankokin yaki sun doshi zirin Gaza, yayin da ake kyautata zaton cewa Isra'ila zata kai farmakin soja a bayan harin kunar-bakin-wake na ranar talata.

Kungiyar Hamas ta mashu kishin Falasdinu, wadda ke da hedkwata a zirin na Gaza, ta dauki alhakin kai wannan hari na ranar talata.

A ranar alhamis majalisar zartaswar Isra'ila ta bada iznin kai farmakin sojan.

Shugaban hukumar tsaro na Falasdinawa a zirin Gaza, Janar Abdul-Razaq al-Majayida, ya ce yana tsammanin Isra'ila zata kai farmaki a ko da wane lokaci daga yanzu.

Shugaba Bush ya ce abin karfafa guiwa ne kama 'yan kungiyar Hamas su 16 da hukumomin Falasdinawa suka yi. Mr. Bush ya ce tsawon lokacin ad zasu yi a kurkuku zai zamo babban gwaji na irin kudurin shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat.

XS
SM
MD
LG