Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Likud Ta Ki Yarda Da Ra'ayin Kafa Kasar Falasdinu - 2002-05-13


Jam'iyyar Likud mai mulkin Isra'ila, ta ki yarda da shawarar firayim minista Ariel Sharon, ta amince da wani kudurin da ya ki yarda da ra'ayin kafa kasar Falasdinu.

Jiya lahadi 'ya'yan jam'iyyar suka amince da wannan kuduri da gagarumin rinjaye a birnin Tel Aviv, a bayan da suka ki yarda da rokon da Mr. Sharon yayi musu na su jinkirta jefa kuri'ar.

Ana daukar wannan kuri'a a zaman shan kashi ga Mr. Sharon, wanda yayi kashedin cewa wannan kuduri nasu zai raunana Isra'ila a fagen diflomasiyya. Kuri'ar, nasara ce ga tsohon firayim minista Benjamin Netanyahu, wanda ya ce kafa kasar Falasdinu zai yi barazana ga rayuwar Isra'ila a zaman kasa.

Magoya bayan Mr. Netanyahu sun fara gabatar da wannan kuduri a watan Satumbar bara, a bayan wani jawabin Mr. Sharon, inda ya ce Isra'ila tana son bai wa Falasdinawa "yiwuwar kafa kasarsu."

Babban jami'in shawarwari na Falasdinawa, Saeb Erakat, ya ce wannan kuri'a ta 'yan Likud, ta gurgunta kokarin da ake yi na farfado da shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG