Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe Mutane Uku A Fadan Siyasa A Madagascar - 2002-05-14


An kashe mutane akalla uku a kasar Madagascar, a wata sabuwar arangama a tsakanin magoya bayan mutane biyun da kowannensu ke ikirarin cewa shine shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya ambaci gidan rediyon kasar yana fadin cewa an raunata wasu mutanen da dama a lokacin da tashi hankali ya barke, bayan farmakin da magoya bayan dadadden shugaba Didier Ratsiraka suka kai kan 'yan kabilar Merina, wadanda suke zargi da nuna goyon baya ga shugaban jeka-na-yi-ka Marc Ravalomanana.

Gidan rediyon ya ce an gwabza wannan fada a garin Mahajanga mai tashar jiragen ruwa a arewa maso yammacin kasar, inda kuma ake dauka a zaman tungar Mr. Ravalomanana.

Tun cikin watan Janairu mutanen biyu suke gwagwarmayar neman ikon mulkin Madagascar. Mr. Ravalomanana ya kafa mulkinsa a Antananarivo, babban birnin kasar, yayin da Mr. Ratsiraka ya kafa tasa cibiyar mulkin a Toamasina, babbar tashar jiragen ruwan kasar.

A bayan da aka sake kidaya kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa na watan disamba, an bayyana Mr. Ravalomanana a zaman wanda ya lashe zaben, aka kuma rantsar da shi a zaman shugaba a ranar 29 ga watan Afrilu.

Amma Mr. Ratsiraka ya ki yarda ya mika masa mulki. Ya zargi alkalan da suka sake kidaya kuri'un da cewa sun fi kaunar Mr. Ravalomanana.

XS
SM
MD
LG