An shirya tsohon shugaban Amurka, jimmy carter, zai yi jawabin da za a nuna shi kai tsaye a lokacin da yake yi ga al'ummar Cuba ta cikin telebijin din kasar, a yau talata, a yayin da yake ci gaba da ziyara mai dimbin tarihi a wannan tsibiri mai bin tafarkin Kwaminis.
An shirya zai gabatar da wannan jawabi daga Jami'ar Havana, a bayan ya tattauna da manoman kasar ta Cuba, ya kuma ziyarci wani asibitin kula da masu fama da cutar AIDS.
Shugaba Fidel Castro na Cuba ya ce tsohon shugaban na Amurka yan da 'yancin yin duk sukar da yake son yi.
Fadar White House, da 'yan majalisar dokoki da dama da kuma kungiyoyin 'yan kasar Cuba dake zaman gudun hijira a nan Amurka duk sun yi kira ga Mr. Carter da ya takali batun kare hakkin Bil Adama da dimokuradiyya a lokacin ziyrara tasa.
A jiya litinin, Mr. Carter ya gana da biyu daga cikin sanannun 'yan adawar Cuba, kuma yana shirin ganawa da karin masu adawa da gwamnatin Cubar a ranar alhamis.