Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sa Ran Masu Jefa Kuri'a Zasu Fito Da Yawa Yau Talata A Saliyo - 2002-05-14


Jami'an zabe sun yi hasashen cewa masu kada kuri'a za su fito sosai yau talata, a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a karon farko a kasar Saliyo, tun bayan kawo karshen kazamin yakin basasar da aka fafata na tsawon shekaru goma.

Galibi, jama'a suna hasashe cewa, shugaban Saliyon na yanzu, Ahmed Tejan Kabbah na jam'iyyar dake mulki, zai lashe zaben na yau. Duk da haka, jam'iyyar R-U-F ta tsohuwar kungiyar 'yan tawaye masu da'awar yin juyin-juya hali, ta ce, tana fatar yin gagarumin tasiri a zaben.

'Yan tawaye sun kauracewa zabubbukan da aka gudanar a kasar ta Saliyo cikin shekarar 1996, sannan suka yayyanke hannuwan wasu daga cikin mutanen da suka jefa kuri'unsu a matsayin horo na kada kuri'un da suka yi.

An kwance damarar 'yan tawayen, tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar a farkon wannan shekarar. Sun kuma gabatar da Mr. Pallo Bangura, a zaman dan takararsu na zaben shugaban kasar na yau talata.

Yanzu haka dai, ana daukar Mr. Ernest Koroma na jamiyar "All People's Congress" a zaman dan takarar da zai fafata sosai da shugaba Kabbah.

An karfafa matakan tsaro a kasar ta Saliyo, sojoji da 'yan sanda suna yin sintiri a tasoshin zabe, karkashin sa idanun dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

An bada rahoton jikkata wasu jama'a ranar asabar, bayan wata arangama da ta kaure a tsakanin magoya bayan shugaba Tejan Kabbah da kuma na jam'iyyar R-U-F.

A jiya litinin ne, Babban Magatakardar MDD, Kofi Annan, ya bayyana wannan kuri'a da za a kada yau a Saliyo, da cewa wani gagarumin ci gaba ne. Ya yi kira ga al'ummar kasar da su kada kuri'unsu cikin lumana tare da yin hakuri da juna.

XS
SM
MD
LG