Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Gudanar Da Taron Sasanta Al'ummar Somaliya - 2002-05-17


Kenya tana shirin karbar bakuncin wani taron sasantawa na al'ummar kasar Somaliya. Wannan taron, wanda watakila ma tun a watan gobe na Yuni za a fara shi, yunkuri ne na kawo karshen fada tsakanin sassan da ba su ga-maciji da juna a Somaliya.

Wakiliyar Muryar Amurka a birnin nairobi, ta ce jami'an Kenya sun kira taron 'yan jarida jiya alhamis, inda suka bayyana irin matakan da ake dauka na lallashin zuriyoyin Somaliya masu fada da juna kan su halarci wannan taron.

Ta ce jami'ai a Nairobi, sun ce idan Allah Ya kai mu ranar litinin wannan mai zuwa, jami'ai daga kasashen Kenya da Ethiopia da Djibouti, watau kasashen dake yin makwabtaka da Somaliya, zasu tafi can.

Ministan harkokin wajen Kenya, Marsden Madoka, ya ce zasu gana da dukkan shugabannin jinsuna da zuriyoyin Somaliya domin tattauna wannan taro na Nairobi, yana mai cewa... ACT: MADOKA: “We will visit every single area where we feel there is some group or some faction leader who needs to be brought on board.....”

Ya ce "zamu ziyarci kowane yankin kasar ta Somaliya inda muke jin cewa akwai wata kungiya ko kuma wani shugaban jinsin da ya kamata mu shigar cikin taron. Idan har akwai bukatar haka, wakilanmu zasu zauna har tsawon makonni biyu a Somaliya, muhimmin abu dai shine mu tuntubi kowa da kowa. Idan mun zaga, zamu ringa tambayarsu ko yaya suke hangen Somaliya nan gaba? Wani irin tsarin gwamnati suke so? Suna son hadaddiyar kasar Somaliya? Ko Mulki irin na tarayya? Wadannan abubuwa sune zasu taimaka mana wajen tsara taron, in ji ministan harkokin wajen Kenya."

An zabi Kenya domin ta gudanar da taron a lokacin wani taron kolin shugabannin kasashen Afirka ta gabas da aka yi a watan janairu.

Shekaru biyu da suka shige, an kafa sabuwar gwamnati a Somaliya, wadda ita ce ta farko cikin shekaru kusan 10 a Somaliya, amma har yanzu yankuna kadan ne kawai suke karkashin ikon gwamnatin. Sauran sassan kasar suna hannun kungiyoyi da jinsuna masu yakar juna.

A cikin 'yan makonnin nan, an samu karuwar fadace-fadace a tsakanin wadannan kungiyoyi. A yankin Gedo na kudu maso yammacin kasar, masu kawance da Gwamnatin Rikon Kwarya ta kasa, wadda take rike da Mogadishu babban birnin kasar, suna yakar kungiyoyi kawayen Majalisar Sasantawa da Maido da Diyaucin Kasa, wadda ita kuma ke samun goyon bayan kasar Ethiopia. A yankin Puntland na arewa maso yammacin kasar kuma, fitina ta sake barkewa a tsakanin wasu kungiyoyi biyu da suke neman ikon mallakin wannan dan karamin yankin da ya bayyana cin gashin kansa.

XS
SM
MD
LG