Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga Gwamnatin Nijeriya Da Ta Wargaza Kungiyar 'Bakassi Boys' - 2002-05-20


Wata kungiyar kare hakkin bil Adama mai hedkwata a New York, da kuma wata kungiyar a Nijeriya sun yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta rushe, ta kuma haramta kungiyoyin banga masu samun daurin-gindin gwamnatocin jihohi a kasar.

A cikin wata takarda mai shafi 45 da aka wallafa a yau litinin, kungiyar "Human Rights Watch" da Cibiyar Wayar da Kai Game da Hanyoyin Tabbatar Da Bin Doka da Oda ta Nijeriya, sun ce wannan kungiyar 'yan banga ko 'yan daba mai suna "Bakassi Boys" ta 'karkashe mutane da yawa ba ta hanyar da doka ta tanada ba, sannan ta gana ma wasu daruruwa azaba, ko ta tsare su haka siddan.'

Kungiyoyin guda biyu, suka ce gwamnatocin jihohi suna kyale wadannan kungiyoyi suna yin abinda suka ga dama, a wasu lokutan ma sukan fito suna goyon bayan irin danyen aikin da kungiyoyin dabar suke aikatawa.

Suka ce gwamnatocin wasu jihohin Nijeriya, sun samar da ofisoshi, da tufafin aiki, da motoci, har ma da biyan albashin wadannan 'yan daba.

Kungiyoyin biyu masu rajin kare hakkin bil Adama sun yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta rushe wannan kungiya ba tare da wani jinkiri ba, ta kuma kwace makaman membobinta.

An kafa kungiyar "Bakassi Boys" a shekarar 1998 domin magance matsalar yawan fashi da makami, kuma tana gudanar da ayyukanta ne a jihohin Anambra da Abia da Imo a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG