Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'Amnesty' Ta Tuhumi Gwamnatocin Kasashen Afirka Da Kungiyoyin 'Yan Tawaye Da laifin Keta Hakki - 2002-05-29


Wata sananniyar kungiyar kare hakkin bil Adama ta ce gwamnatoci da kuma kungiyoyin 'yan tawaye a kasashen Afirka da dama suna gudanar da ayyukan keta hakkin Bil Adama dake shafar miliyoyin jama'a.

Cikin rahoton da ta bayar jiya talata, kungiyar "Amnesty International" ta ce wadannan ayyuka na keta hakki sun hada da kama mutane, da tsare su, da sace mutane, da gana azaba, da fyade, da kisa da kuma 'bacewa'.

Wannan rahoto na kungiyar mai hedkwata a birnin London, ya kunshi bayanin abubuwan da suka faru daga watan Janairu zuwa watan Disamba na shekarar da ta shige.

Kungiyar ta zana sunayen kasashen da ta ce har yanzu ana ci gaba da daure mutane a saboda dalilai na siyasa. Kasashen sune: Angola, Burundi, Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, Cote D'Ivoire (Ivory Coast), Equatorial Guinea, Eritrea, ethiopia, Guinea-Conakry, Guinea-Bissau, Kenya, Rwanda, Swaziland, Sudan da kuma Zimbabwe.

XS
SM
MD
LG