Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Britaniya Dake Afghanistan Sun Kaddamar Da Sabon Farmaki - 2002-05-30


Britaniya ta kaddamar da sabon farmakin soja a yankin gabashin Afghanistan, domin hana mayakan al-Qa'ida da na Taleban sake shiga Afghanistan daga Pakistan.

Wani kakakin sojojin Britaniya a Afghanistan, ya ce an girka sojojinsu kimanin 300 kusa da bakin iyaka da Pakistan cikin makon nan, domin yin sintiri a kasa da kuma ta sama.

Za a shafe makonni da dama ana gudanar da wannan aikin soja domin hanawa mayakan Taleban da na al-Qa'ida sukunin gurgunta babban taron majalisar kasa na Afghanistan da za a yi cikin wata mai zuwa a Kabul.

A halin da ake ciki, 'yan sandan Pakistan tare da taimakon jami'an hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya a nan Amurka sun kama wasu mutane biyun da ake jin cewa 'ya'yan kungiyar al-Qa'ida ne, lokacin da suka kai sumame a birnin Peshawar dake bakin iyaka a arewa maso yammacin kasar.

XS
SM
MD
LG