Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'addar 1993 Sun Yi Niyyar Dasa Bam Ne A Unguwar Yahudawa Na Birnin New York... - 2002-06-03


Wani dan kasar Iraqi, wanda ya amsa cewa ya taimaka wajen kai harin farko kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a 1993, ya ce niyyarsu ta farko ita ce ta dasa bam a unguwannin yahudawa na birnin New York.

Cikin hirar da yayi da gidan telebijin na CBS na nan Amurka, Abdul-Rahman Yasin ya ce mutumin da shine kanwa uwar gami wajen kulla wannan harin, wanda kuma aka samu da laifi, Ramzi Yousef, yayi niyyar kai hare-haren bam ne tun farko kan unguwannin yahudawa. Amma kuma ya ce daga baya Yousef ya yanke shawarar cewa kai hari kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya zai fi sauki, zai kuma kashe yahudawa fiye da na unguwannin.

Yasin ya ce ya taimaka wajen harhada sinadaran bam din da ya fashe a garejin dake karkashin ginin, ya kashe mutane 6, ya raunata wasu fiye da dubu daya.

Gidan telebijin na CBS ya ce a yanzu dai, Yasin yana daure a birnin bagadaza, inda ya gudu a bayan harin.

XS
SM
MD
LG