Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Zata Kara Da Ireland A Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Na Duniya... - 2002-06-05


Kece rainin da za a yi a tsakanin Jamus da Ireland a yau laraba, shine babban abin kallo ga wasu, a ci gaba da gasar cin kofin duniyar da ake yi a Japan da Koriya ta Kudu.

A tamaular farko da ta yi a wannan gasa, Jamus tayi kaca-kaca da 'yan wasan Sa'udiyya da ci 8 da wofi. Ireland kuma ta kwaci kanta da kyar, ta yi kunnen doki da 'yan wasan Kamaru.

Kasashe hudu kuma, zasu fara buga tamaularsu a yau larabar. A birnin Kobe a Japan, Tunisiya zata gwabza da 'yan kasar Rasha. 'Yan wasan kasashen biyu da dama suna fama da rashin koshin lafiya saboda rauni.

Amurka zata kara da kasar Portugal, daya daga cikin kasashen da masu fashin bakin tamaula, suke zaton suna da damar lashe wannan kofi. Shahararren dan wasan Portugal, Luis Figo, ya ce ya kosa ya shiga filin tamaula, a bayan da ya murmure daga raunin da ya jinginar da shi a gefe tun watan Fabrairu.

XS
SM
MD
LG