Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mueller Ya Ce Tilas Hukumar FBI Ta Yi Sauyi - 2002-06-07


Darektan hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya a Amurka, FBI, Robert Mueller, ya yarda cewa tilas ne hukumar tasa ta gudanar da muhimman sauye-sauye domin gudanar da babban nauyin da ya rataya a wuyarta na hana abkuwar hare-haren ta'addanci nan gaba.

Wakilan kwamitin shari'a na majalisar dattijan Amurka sun yi wa Mr. Mueller tambayoyi jiya alhamis. 'Yan majalisar sun yi tambayoyi masu zafi kan dalilin da ya sa hedkwatar hukumar ta FBI ba ta dauki matakai ba, dangane da bayanai masu muhimmanci da jami'anta na rassa suka aiko kafin hare-haren 'yan ta'adda na 11 ga watan Satumba.

Jami'ar hukumar FBI, Coleen Rowley, ta gana da 'yan majalisar a asirce shekaranjiya laraba, a bayan da ta zargi hedkwatar hukumar da laifin gurgunta wani muhimmin bincike.

Jiya alhamis a bainar jama'a kuma, Ms. Rowley ta shaidawa kwamitin cewa tsarin matakan da ake bi wajen yanke shawara a hukumar ta FBI yana kashe kwarin guiwar jami'ai masu bincike.

XS
SM
MD
LG