Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzoma Kan Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Duniya A Rasha Ta Kashe Mutum Guda - 2002-06-10


Hukumomi a birnin Moscow sun yanke shawarar daina nuna kwallon kafar cin kofin duniya a manyan allunan majigi, a bayan da dubban 'yan kallo suka tayar da tarzomar da ta kashe mutum guda, ta raunata wasu da dama.

Wannan tarzoma ta barke jiya lahadi a tsakiyar birnin Moscow, a lokacin da kasar Japan ta doke Rasha da ci daya mai ban haushi a karawar ad suka yi a rukuninsu.

Kafofin labaran Rasha sun ce mutane akalla 20 sun ji rauni a wannan tarzoma. 'Yan sanda suka ce 'yan kallo, wadanda suka yi ta shan barasa a duk tsawon lokacin da ake nuna wasan, sun kona motoci da dama, suka mirgina wasu da dama.

XS
SM
MD
LG