Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Shirin Kammala Taron Kolin Samar Da Abinci Na Duniya Ba Tare Da An Cimma Wani Abu Ba - 2002-06-13


Yau alhamis za a kawo karshen taron kolin abinci na duniya na kwanaki hudu, wanda MDD ta shirya a birnin Rum, ba tare da an samo ahnyar fuskantar matsalar yunwa a duniya ba.

Wannan taro, ya samo asali ne daga taron kolin 1996t, inda kasashe fiye da 180 suka yi alkawarin cewa nan da shekarata 2015, zasu rage yawan mutanen da suke fama da yunwa a duniya da rabi, daga miliyan 800 zuwa miliyan 400. Amma kuma jami'ai suka ce har yanzu kusan babu wani abinda ya canja.

Shugabanni 80 suke halartar wannan taron koli na Rum daga kasashe masu tasowa na Afirka, ad Asiya da Amurka ta Kudu. Amma kuma shugabannin kasashe biyu ne tak masu arzikin masana'antu suka bayyana a wurin taron, watau mai masaukin baki firayim minista Silvio Berlusconi na Italiya, da kuma firayim ministan kasar Andalus (Spain), Jose Maria Aznar, wanda yake wakiltar tarayyar Turai.

Wasu 'yan rajin kawar da yunwa a duniya sun ce rashin zuwan shugabannin kasashe masu arziki ya gurgunta taron. A yau alhamis taron zai bayar da sanarwar karshen taro kan shirye-shiryen kawar da yunwa a duniya nan gaba.

A halin da ake ciki, shugabannin kasashen Afirka dake halartar taron kolin sun amince da wani shirin radin-kai na kyale 'yan'uwansu suna auna irin kamun ludayinsu kan mulki, a wani bangare na sabon shirin neman kasashen waje su zuba jari a nahiyar Afirka.

Manyan wakilan wannan sabuwar Kawancen Raya Kasashen Afirka, ko NEPAD, mai wakilai 15, zasu dauki wannan daftari su kai gaban taron kungiyar kasashe 8 masu arzikin masana'antu da za a yi nan gaba cikin wannan wata a Canada.

XS
SM
MD
LG