Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld Zai Gana Da Shugaba Musharraf Yau Alhamis - 2002-06-13


Sakataren tsaron Amurka, Donald Rumsfeld, zai gana yau alhamis da shugaba Pervez Musharraf na Pakistan a birnin Islamabad, a wani bangare na kokarin da Amurka take ci gaba da yi na kawo akrshen zaman tankiya tsakanin Indiya da Pakistan a bakin iyakarsu.

A jiya laraba, Mr. Rumsfeld ya gana da jami'an Indiya a birnin New Delhi, cikinsu har da firayim minista Atal Behari Vajpayee. Ya ce sun tattauna batun yin amfani ad wasu na'urorin sunsuno mutane da Amurka take kerawa domin sanya idanu a kan 'yan kishin Kashmir masu tsallakawa daga Pakistan zuwa cikin bangaren Indiya na Kashmir.

Batun wannan yanki na Kashmir, shine ke haddasa gaba a tsakanin kasashen biyu masu makaman nukiliya, wadanda suka girka sojoji fiye da miliyan daya a bakin iyakarsu.

Haka kuma, Mr. Rumsfeld ya ce ya ga alamar cewa 'yan ta'addar al-Qa'ida suna kai da komowa a bakin iyakar Indiya da Pakistan a Kashmir. Sai dai kuma sakataren tsaron an Amurka ya amsa cewa ba ya da wata kwakkwarar shaida kan yawa ko kuma inda mayakan na al-Qa'ida suke a cikin Kashmir.

XS
SM
MD
LG