Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Mazan Jiya Sun lashe Zaben Faransa... - 2002-06-17


Kawancen 'yan mazan jiya masu sassaucin ra'ayi na shugaban kasar Faransa, Jacques Chirac, ya samu nasarar da babu tababa cikinta, a zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi a kasar a jiya lahadi, a yayin da jam'iyyar "National Front" ko "Front Nationale" ta masu tsananin ra'ayin kishin kasa, ta kasa samun ko da kujera daya.

Bayan an kirga kusan dukkanin kuri'un da aka kada, 'yan mazan jiyan dake cikin kawancen shugaba Chirac, sun samu kujeru 392, al'amarin da ya ba su cikakken rinjaye a majalisar dokokin kasar mai kujeru 577, bayan ta yi shekaru biyar gam a hannun 'yan gurguzu.

'Yan gurguzun kasar Faransa sun samu kujeru 138, a yayin da wasu jam'iyyu masu ra'ayin canji suka samu kujeru 36.

Har yanzu akwai sauran kujeru da dama wadanda ba'a fadi wadanda suka lashe su ba.

Ga dukkan alamu, shugaban gwamnatin Jacques Chirac, Firayim minista Jean-Pierre Raffarin, mai ra'ayin 'yan mazan jiya, yayi shirin gudanar da majalisar dokokin na wasu shekaru biyar nan gaba. Wannan nasara da kawancen shugaba Jacques Chirac ya samu, ta kawo karshen wani matsayi na rabuwar mulki tsakanin gwamnati da shugaba.

XS
SM
MD
LG