Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Tayi barin Wuta Kan Cibiyoyin Falasdinawa - 2002-06-20


Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama kan cibiyoyin Falasdinawa a zirin Gaza, a bayan wani harin kunar-bakin-waken da ya kashe mutane akalla 7 a birnin Qudus. Wakilin Muryar Amurka, Ross Dunn, ya ce wannan harin shine na biyu cikin kwanaki biyu a birnin.

Jiragen sama masu saukar ungulu sun cilla makamai masu linzami kan cibiyoyi a cikin birnin Gaza da garin Khan Younis dake kudancin zirin Gaza. Hare-haren ta sama, sun biyo bayan hare-haren bam biyu na kunar-bakin-wake a Qudus, inda mutane akalla 26 suka sheka barzahu, wasu fiye da 100 suka ji rauni. Kakakin gwamnatin Isra'ila, Daniel Seaman, wanda a lokuta da dama ake kira domin ya ziyarci inda aka kai hare-hare, ya ce ya girgiza da abinda ya gani.

Kakakin na Isra'ila ya ce lokaci yayi da za a fadawa shugaban Falasdinawa, Yasser Arafat, cewar koda yake 'yan Isra'ila ne suke dandana kudarsu a yanzu, karshenta dai Falasdinawa ne zasu yi da na-sanin irin wadannan hare-haren.

An rufe wurin da aka kai harin bam din, abinda ya haddasa cunkoson ababen hawa. Jirage masu saukar ungulu na 'yan sanda sun yi ta shawagi a sama. Ma'aikatan agaji sun yi ta kai gwauro da mari, suna tattara abubuwan da suka rage na gabobin jama'a cikin bakaken laida.

A bayan hare-haren, Isra'ila ta bada sanarwar cewa zata kama ta rike yankunan Falasdinawa har sai an kawo karshen wadannan hare-hare na durawa mutane ruwa a ciki.

A jiya laraba, sojojin Isra'ila sun kama wasu garuruwa biyu dake karkashin mulkin Falasdinawa, Jenin da Qalqilya a yankin yammacin kogin Jordan. An gwabza kazamin fada a garin Qalqilya a yayin ad sojojin Isra'ila suka fara farautar 'yan kishin Falasdinu.

XS
SM
MD
LG