Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tana Fadada Shirin Bada Tukuici Domin Farauto Masu Kisa Na Rwanda - 2002-06-20


Amurka tana fadada wani shirinta, wanda a karkashinsa zata bada tukuicin kudin da ya kai har dala miliyan 5, ga duk wanda ya tsegunta mata wani bayanin da zai kai ga kamo wadanda ake tuhuma da aikata kashe-kashe na kare-dangi a Rwanda.

Jami'an Amurka suna fatan cewa kamo wadannan 'yan kasar Rwanda, wadanda aka yi imanin cewa wasunsu sun buya a kasar Kwango Kinshasa, zai taimaka wajen gaggauta kawo karshen yakin da ake yi a can.

Wannan shirin bada tukuici na ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ya samu nasara sosai domin ya taimaka wajen kamo wadanda ake tuhuma da aikata ta'addanci da wadanda ake zaton sun aikata laifuffukan yaki a yankin tsaunukan Balkans.

A yanzu ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka tana kara azamar wani shirinta wanda ba kowa ya san da shi sosai ba, wanda aka kaddamar shekara guda da ta shige, domin kamo mutanen da ake farauta dangane da kisan kare dangi da aka yi a Rwanda a 1994.

Jakadan Amurka na musamman mai kula da batutuwan da suka shafi laifuffukan yaki, Pierre-Richard Prosper, ya kaddamar da wannan sabon gangami cikin makon da ya shige a birnin Nairobin Kenya, inda jami'an Amurka da na Kenya suka rarraba hotunan da aka buga na neman wani attajiri dan kabilar Hutu mai suna Felicien Kabuga, wanda ake tuhuma da laifin yin amfani da kudinsa wajen haddasa kashe-kashen na kare-dangi a Rwanda.

Har ila yau, a can birnin Rum kuma, Mr. Prosper ya gana da shugaba Paul Kagame na Rwanda da shugaba Joseph Kabila na Kwango, wanda ya gayyaci jakadan na Amurka da ya ziyarci birnin Kinshasa a wata mai zuwa domin kaddamar da babban gangami na rarraba hotunan mutanen da ake nema. Wannan gangami na Kwango Kinshasa za a kaddamar da shine da nufin kamo wasu mutane 8 wadanda kotun duniya dake bin kadin laifuffukan yaki a Rwanda take tuhuma.

An yi imanin cewa mutanen takwas, shugabannin wata kungiyar da ta bai wa kanta sunan "Rundunar Kwatar 'Yancin Rwanda", sun buya a cikin Kwango Kinshasa. A bayan rawar da suka taka a kashe-kashen da aka yi a Rwanda, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce haka kuma suna samar da kudi, da rura wuta tare da tallafawa yakin da ake yi yanzu haka a Kwango Kinshasa.

Cikin tattaunawar da yayi da Muryar Amurka, jakada Prosper ya ce damke wadannan Hutawa 'yan tsagera su takwas zai taimaka wajen kawo karshen yakin Kwango Kinshasa a saboda zai kawo janye sojojin Rwanda daga gabashin kasar.

Jakada Prosper, ya kara da cewa, "...Shugaba Kagame ya bayyana mana a fili cewa daya daga cikin dalilan da suka sa sojojinsa suke cikin Kwango Kinshasa, shine farauto 'yan kisan kare-dangin da suka buya a can suna tayar da fitina. Har zuwa yau, wadannan mutane suna sa hannu cikin fitinun dake faruwa. A saboda haka, mun yi imanin cewa idan muka kamo wadannan mutane muka mika su ga wannan kotu, zamu kawar da barazanar tsaron da kasar Rwanda take fuskanta daga gare su. Wannan kuma zai sanya Rwanda ta fara janye sojojinta daga Kwango, ka ga zaman lafiya zai samu ke nan...."

Wani jami'in Amurka ya shaidawa 'yan jarida cewa akwai hannun shugabannin rundunar 'yan kwatar 'yancin Rwandan a wajen sacewa da kashe baki 'yan yawon shakatawa su 8, cikinsu har da Amurkawa biyu, a wani gandun dabbobi dake bakin iyakar Kwango da Uganda a shekarar 1999.

Mutumin da Amurka take farauta a Nairobi dai, Felicien Kabuga, babban attajiri ne wanda ke da harkokin kasuwanci a kasashen Afirka da dama. Jami'in na Amurka ya ce a shekarar 1994, Mr. Kabuga ya biya kudi aka yi ta watsa kiraye-kirayen da a karkashe Tutsawa da Hutawa masu sassaucin ra'ayi, sannan kuma ya sayi makamai da khaki ma 'yan dabar kabilar Hutu.

Jami'in ya ce tuni har wannan kyamfe na Kenya ya fara samun nasara, inda hukumomi suka samu bayanai ta wayar tarho da kuma ta duniyar gizo har 250 kan wuraren da Mr. Kabuga yake. A karshen makon da ya shige ma, 'yan sandan Kenya sun kama wani mutumin da yayi kama da Mr. Kabuga a bayan da wani mai son samun wannan tukuici ya tsegunta musu, amma daga baya sai aka gano cewar ba shi ba ne.

XS
SM
MD
LG